Mazauna kauyen sun ce 'yan Boko Haram din sun kuma sace mutane da yawa.
A cewarsu, mutanen da aka sace sun hada da maza da mata.
An kai harin ne tun ranar Lahadi amma sai yanzu aka samu labari saboda rashin hanyoyin sadarwa.
Har yanzu dai babu cikakken bayani game da adadin mutanen da aka kashe ko aka sace daga kauyen.
Jihar ta Borno dai na ci gaba da fuskantar hare-haren kungiyar ta Boko Haram, duk da cewa tana daga cikin jihohin da ke karkashin dokar ta-baci.ABAN